Tawagar masu shiga tsakani a Libya

A kasar Libya, ana ci gaba da tafka fada a garin nan mai matukar muhimmanci wato, Ajdabiya.

Dakarun gwamnati sun kaddamar da karin hare hare a garin, wanda ke hanun yan tawaye, wanda kuma daga shi ne sai birnin Benghazi, matattarar yan adawar.

A yammacin kasar ta Libya, dakarun kungiyar NATO, sun kai hare hare ta sama kan dakarun gwamnati , wadanda suka yi ma garin Misrata kofar-rago.

Idan an jima a yau ne ake sa ran wata tawagar masu shiga tsakani daga kasashen Afirka zata sauka a birnin Tripoli.