Dokar hana sa niqab a Faransa ta fara aiki

'Yan sanda a Faransa sun kama wasu mata biyu, a lokacin wata 'yar zanga-zangar da aka yi a gaban wani coci a birnin Paris, don kokawa da wata sabuwar dokar da ta hana rufe fuska ruf a bainar jama'a.

An kama matan ne saboda sun shiga zanga zangar da aka haramta.

Akalla dayarsu tana sanye da niqab - ko malullubin fin da ya rufe dukan fuska, wanda hukumomin Faransa suka haramta daga yau.

A cewar gwamnatin Faransar, niqab din yana danne hakkin mata.

To amma a ganin 'yan adawa, sabuwar dokar ta keta hakkin bil'adama.