Yan tawayen Libya sun yi watsi da shirin zaman lafiya na AU

'yan adawar da ke mulkin ma fi yawan gabashin Libya sun yi watsi da wani shirin zaman lafiya da masu shiga tsakani na kungiyar tarayyar Afrika ta AU su ka gabatar.

'yan adawar sun ce shirin na kungiyar tarayyar Afrika ta AU ya gaza biyan bukatun al'umar Libya, kasancewar bai baiyana makomar kanar Ghaddafi da 'ya'yansa ba.

A baya dai, tawagar ta AU ta ce gwamnatin Libya ta amince da shirin, tare kuma da batun tsagaita wuta.

Sai dai ministan hulda da kasashen waje na Italiya, Franco Frattini ya ce kasasarsa na goyon bayan shirin na kungiyar AU.

Yace; "su na aiki tukuru wurin warware rikicin siyasar kasar wanda bai kunshi dorewar Ghaddafi a Libya ba. Wannan kuma shi ne daidai. Don haka mu ke goyon bayansu."