Jega zai gana da kwamishinonin zabe na jihohi

Image caption Masu kada kuri'a a Najeriya

A Najeriya, a yau ne ake sa-ran shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Attahiru Jega zai yi wani zama da kwamishinonin zaben hukumar da ke jihohin kasar a Abuja.

Manufar taron dai ita ce a duba hanyar gudanar da zaben shugaban kasar da ke tafe ta yadda zai kasance karbabbe.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da zabukan `yan majalisar dattawa da na wakilan kasar.

Sai dai, duk da cewa an yaba da kokarin da hukumar zaben kasar ta yi wajen gudanar da zaben, an bayyana cewa zaben ya ci karo da wasu matsaloli da suka hada da bacewar sunayen masu zabe a wasu mazabu, da kuma satar akwatunan zabe.

Zaben shugaban kasar dai ya na da muhimmancin gaske, musamman ma yadda kasashen duniya suka zuba wa Najeriya ido don ganin yadda zai kasance.