Kusa zai halarci wani taro kan Libya

Musa Kusa
Image caption Musa Kusa, tsohon Ministan harkokin wajen Libya

Tsohon ministan hulda da kasashen waje na Libya, Moussa Koussa, wanda ya tsere zuwa Burtaniya a watan jiya, na kan hanyarsa ta zuwa Doha a kasar Qatar.

Zai je can ne domin baiwa jami'an kasar shawara gabannin wani muhimmin taron kasa da kasa kan makomar Libya.

Gwamnatocin Burtaniya da Faransa dai sun bukaci sauran kasashen da ke cikin kawancen NATO da su kara kokari wurin kare farar hula a Libya.

Sakataren hulda da kasashen waje na Burtaniya William Hague ke cewa ya zama wajibi mu kara kokarinmu a cikin NATO.

Dalili ke nan da Birtaniya ta bada karin jiragen yakin da ka iya kai hari kan cibiyoyin da ke barazana ga al'ummar Libya.