Alamun baraka tsakanin dakarun NATO

Gwamnatocin kasashen Birtaniya da Faransa suna kukan cewa, sauran mambobin kungiyar tsaron NATO ba sa kawo gudunmawa sosai, a farmakin sojan da ake kaiwa Libiya.

A cewar ministan harkokin wajen Faransa, Gerard Longuet, Faransar da Birtaniyar ne ke kai gwauro su kai mari, wajen tabbatar da takunkumin hana jirage yin shawagi a sararin samaniyar Libiyar.

Makonni biyu da suka wuce ne NATO ta dauki nauyin kare sararin samaniyar kasar ta Libiya.

Ko a kwanakin baya 'yan adawar Libyar sun nuna rashin gamsuwa da ayyukan NATOn.