Jam'iyyar ACN a jihar Jigawa za ta garzaya kotu

Image caption Jami'yyar adawa ta ACN

Jam'iyyun hamayya a jihar Jigawa dake arewacin Nigeria sun yi barazanar kalubalantar nasarar da aka bayyana jam'iyyar PDP ta samu a zabukan majalisar dokokin Nigeria.

Senata Saminu Turaki da ya tsaya takarar dan majalisa datawa karkashin innuwar jamiyyar ACN ya ce an tafka magudi a zabukan wanda ya kai ga bayyana jam'iyyar PDP dake mulkin jahar a matsayin wacce ta lashe dukkanin kujerun da aka yi takara a kansu.

Ya kuma ce jam'iyyarsa za ta garzaya kotu don kalubalantar nasarar da aka bayyana jam'iyyar PDP ta samu a Jihar

Su ma dai sauran jam'iyyun hamayyar jahar ta Jigawa da suka yi wani taron manema labarai a jiya sun bayyana cewa zasu mikawa hukumar zabe korafe korafensu.