Harin bom ya kashe mutane 10 a Afghanistan

Haji Malik Zarin
Image caption Haji Malik Zarin (na tsakiya) tsohon mayaki ne a Afghanistan

Dan kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 10 a wani hari da ya kaiwa wasu shugabannin kabilu a Gabashin Afghanistan.

Wani shugaba a yankin da ke goyon bayan shugaba Karzai Haji Malik Zarin, na daga cikin wadanda suka mutu a harin kusa da kan iyakar kasar da Pakistan. Mr Zarin, wanda na hannun damar shugaba Hamid Karzai ne, ya mutu tare dansa da kuma wasu 'yan uwansa.

Mai magana da yawun kungiyar Taliban ya musanta cewa su suka kai harin, yana mai cewa Mr Zarin na da abokan hamayya. Ofishin shugaba Karzai ya bayyana mutuwar Mr Zarin da cewa ba karamin rashi ba ne.

Wakilin BBC a Kabul Quentin Sommerville, ya ce yankin da lamarin ya faru ya saba fuskantar irin wadan nan hare-hare.