Matsalar fari ta kunno kai a Cuba

Image caption Shugaba Raul Castro na cuba

Kasar Cuba na fama da fari wanda ta yi shekaru hamsin ba ta ga irinsa ba, kuma mutane fiye da dubu dari dake Havana babban birnin kasar, sun dogara ne a'kan tankokin ruwa, domin sha da dafe dafe da wanke wanke.

Matsalar ta faro ne shekaru biyu da suka gabata, kuma a yanzu rumbuna da dama sun ragu da kusan rabin abinda suke da shi a da.

Gwamnztin kasar dai ta fara daukar mataki ta hanyar amfani da motocci wurin samar da agaji ga wuraren da matsalar ta fi kamari.

A yanzu haka jama'a fiye da dubu dari a birnin Havana sun dogara kacokan ne kan motoccin dake dakon ruwa domin samar da ruwan girki da kuma na wanki.

Sai dai mahunkuntan kasar sun ce kusa da kashi sabain cikin dari na bututu ruwan kasar dake samar da ruwan sha a babban birnin na yoyo kuma na matukar bukatar gyra.