Taron masu adawa da Kanar Gaddafi

Kanar Gaddafi
Bayanan hoto,

Wasu magoya bayan Kanar Gaddafi na zanga-zanga a Tripoli

Nan gaba a ranar Laraba ne ake saran gudanar da wani taro a kasar Qatar, tsakanin kasashen dake adawa da mulkin Kanar Gaddafi a Libya.

Ministocin na sa ran kara kaimi kan gwamnatin, ganin cewa hare-hare ta sama sun kasa durkusar da dakarun kanar Gaddafi.

Kasashen Faransa da Burtaniya kuma na yin kira ga kasashe, da su bada taimakon jiragen saman yaki.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague, ya ce ana samun ci gaba da kuma koma baya akan halin da ake ciki dangane da matakin soja.

Kuma ana bukatar a kara matsawa kasar Libya lamba ta hanyar siyasa da kuma amfani da karfi.

Kasashe da dama da za su halarci wannan taro sun yi amanna cewa ya zama dole ga kanar Gaddafi ya sauka daga mulki kuma suna son kowannen su ya dauki wannan matsaya a sanarwar bayan taron da za'a fitar.

Sai dai yadda za su cimma wannan matsaya ya kasance wani abu me wuya.