Kasashe sun amince su tagaza wa yan tawayen Libya

Kanar Gaddafi Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Wasu magoya bayan Kanar Gaddafi na zanga-zanga a Tripoli

Wakilan kasashen dake adawa da mulkin Kanar Gaddafi a Libya sun amince da samar da wata hanyar bayar da taimakon kudi ga yan tawaye.

Wata sanarwa da suka bayar bayan gungun kasashen yayi wani taro a Qatar, ta ce za a yi amfani da taimakon domin tallafawa abinda suka kira bukatun kudi da na tsare -tsaren yan tawayen na wani gajeren lokaci.

Ba ta yi maganar ko ya Allah za a yi amfani da kudin domin sayen makamai ba.

Sanarwar ta nanata kira ga Kanar Gaddafi da ya sauka, tana mai hakkakewa da cewar ya rasa dukanin wani halacci.

Kuma ta ce kasashen dake da hannu a lamarin sun kudurci daukar dukanin matakan da suka wajaba na kare fararen hula a Libya.

Tun farko Sakataren hulda da kasashen waje na Burtaniya, William Hague yayi kira ga sauran kasashen duniya da su ba da gudunmawa a hare-haren jiragen saman da ake kai wa kasar Libya.