An tsare Hosni Mubarak da 'ya'yansa

Hosni Mubarak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Mubarak ya shafe shekaru talatin yana mulkar Masar

Mai gabatar da kara na Masar, ya umarci a tsare tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak, a daidai lokacin da ake bincikensa kan zargin almundahana da dukiyar kasa.

Rahotanni dake fitowa daga kasar Masar sun ce, an kama 'yayan tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak su biyu, bayanda aka garzaya da mahaifin na su asibiti lokacin da ake masa tambayoyi kan zargin cin hanci da rashawa.

Rahotanni sun ce, an bada umurnin a ci gaba da tsare su na kwanaki 15 tare mahaifin na su domin yi masu tambayoyi game da satar dukiyar kasa.

A halinda ake ciki dai babu tabbas dangane da lafiyar Hosni Mubarak, illa rahoton rashin lafiyarsa da kafar talabijin na kasar ta bayar.

Wani gidan talabijin na kasar ya ce , an tafi da tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak, sashen asibiti da ke bada kulawar gaggawa a asibitin kasa da kasa na Sharm Al-Shaykh, bayanda zuciyarsa ta buga.