Fargaba kan amfani da kudi a lokacin zabe

Zaben Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gangamin yakin neman zabe a Najeriya

A Najeriya a yayin da hankali ya fara karkata kan zaben shugaban kasa da za a yi ranar Asabar mai zuwa, ana ci gaba da nuna shakku kan yiwuwar amfani da kudi domin sauya ra'ayin masu zabe.

Rahotannin da ke fitowa daga sassan kasar bayan kammala zaben 'yan majalisar dokokin kasar, ya nuna cewa an yi amfani da kudade da kayan masarufi da suka hada da abinci da sabulun wanka.

Haka kuma wasu rahotannin ma na cewa a wasu lokutan har sai ansa mutane sun rantse da Alkur'ani mai tsarki don su jefa kuri'arsu ga wani dan takara, lamarin da tuni Malaman addini su ka yi tur da shi.

Kungiyoyi masu sa ido kan zaben Najeriya, sun ce akwai babban aiki a gaban hukumomin tsaron kasar da na zabe dan ganin cewa an dakile al'adar wacce ta saba doka.

Sai dai sun ce za a iya amfani da wayoyin hannu dan daukar hoton yadda ake rabon kudaden ta yadda za su zama shaida ga hukumomi.