Kungiyoyi masu sa ido a kan zaben Najeriya na cigaba da nuna damuwa

Image caption Masu kada kuri'a a Najeriya

A yayinda ya rage yan kwanaki a sake kada kuria a Najeriya, domin zaben shugaban kasa, wata kungiya mai sanya idanu a bisa zabe mai alaka da Cocin Katolika ta nuna damuwa a bisa wasu kurakurai a zaben da aka gudanar na yan majalisar kasa daya gabata.

Wasu daga cikin kura kuran da kungiyar ta ce ta gani sun hada da zabe da yara wadanda basu isa zabe ba ,rashin zuwan masu aikin zabe da wuri da kuma ganin hotunan yan takara a kusa da inda ake kada kuri'a, ko kuma kada kuri'a kusa da offisoshin jamiyyu..

Fada Peter Babangida Audu na cikin wadanda suka sa ido a zaben kuma ya shaidawa BBC cewa abun da su ga da idanunsu ko kadan basu da ce ba.

Ya yi kuma kira ga hukumar zabe me zaman kanta akan ta dauki mataki domin magance wanan matsala don samar da zabe inganci a kasar.