Kungiyar Brics ta yi tir da Nato

Kungiyar manyan kasashe masu tasowa na duniya da ake wa lakabi da BRICS ta yi tur da hare-haren da NATO ke kai wa a Libya.

Da ya ke jawabi a karshen wani taron yini guda a kudancin China, shugaba Medvedev na Rasha ya ce kudirin da majalisar dinkin duniya ta zartar kan batun Libya bai ba da izinin amfani da karfin soji ba.

Ya kuma ce kasashen kungiyar sun ma fi damuwa da yadda dakarun NATOn ke kashe farar hula a hare-haren na su.

Yace, kudirin da majalisar dinkin duniya ta yi ya yi daidai sai dai bai kamata a wuce makadi da rawa ba a kokarin aiwatar da shi.

Wannan kuwa mummunar dabi'a ce a dangantaka tsakanin kasa da kasa.