Buhari da Shekarau suna tattauna hadewa

Buhari, da Ribadu da Shekarau Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ko 'yan hamayyar za su iya hada kai?

A halin yanzu ana can ana tattaunawa tsakanin bangaren Alhaji Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC da kuma Malam Ibrahim Shekarau na ANPP, a kan fidda dan takara shugabancin Najeriya guda daga cikinsu.

Bisa dukkan alamu, a shirye shi Malam Ibrahim Shekarau yake ya bar wa Alhaji Muhammadu Buhari

Jya ne dai wani kokarin cimma yarjejeniyar ya ruguje tsakanin jam'iyyun CPC din ta ACN, inda Nuhu Ribadu zai sauka ya bar wa Buharin, inda batun Mataimakin Shugaban kasa ya zame masu karan tsaye.

A Najeriya, dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar hamayya ta ACN, Malam Nuhu Ribadu, ya ce a iya saninsa jam'iyarsu ta yi kokarin kulla yarjejeniya da jam'iyyar CPC, yana mai dora laifin wargajewar shirin a kan jam'iyyar CPC.

A tattaunawarsa da Nasidi Adamu Yahya, ya ce da jam'iyar CPCn ta amince ta ba su mukamin mataimakin shugabancin kasa, kamar yadda suka nema, da sun tunkari jam'iyar PDP, ba tare da wani shayi ba.

To sai dai a nasa bangaren, dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar hamayya ta CPC, Alhaji Muhammadu Buhari, shi kuma cewa yake, ba bangaren jam'iyyarsu ne ya yi sanadiyar rugujewar shirin hada karfin ba.