Gobara a ofishin Jama'atul Nasril Islam Kaduna

Rahotanni daga Kaduna a Nijeriya na cewa yginin hedkwatar kungiyar Jama'atu Nasril Islam na can na cin wuta.

Da yammacin yau ne wutar ta tashi, kuma ta kone baban dakin taro na hedkwtar.

Babu maganar asarar rayuka. Kuma 'yan kwana-kwana suna can suna kokarin kashe gobarar.

Rahotannin farko sun nuna an sami tashin gobarar ne bisa matsalar wutar lantar da aka samu a ginin.