Amurka da kawayenta sun ce dole kanar Gaddafi ya sauka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Taron ministoccin harkokin wajen kungiyar NATO a Berlin

Kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa sun jaddada bukatar dake akwai ta ci gaba da matsa kaimi kan Kanar Gaddafi, duk da alamun dake nuna rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen kungiyar NATO game da kai hare hare a Libya.

Shugaba Obama da Nicolas Sarkozy na Faransa, da kuma firaministan Birtaniya David Cameron duk sun rubuta wasiku ga manyan jaridu cewa kare fararen hula bai isa ba, dole Kanar Gaddafi ya tafi.

Wakilin BBC ya ce wanan sako ne da ba shi da sassauci kuma yana zuwa ne a dai dai lokacin da ake cigaba da nuna damuwa akan irin salon da yakin Libya ya dauka.

A wani taron ministoccin harkokin wajen kungiyar NATO da akayi a birnin Berlin, Amurka ta ce zata cigaba da taka rawa a kawancen.

Ta kuma amincewa jiragen saman yakin Birtaniya da Faransa su jagorancin kawancen .

Bugu da kari Shugaba Obama zai so su cigaba da yin haka kuma wata kuriar jin ra'ayoyin jama'a na baya baya nan na nuni da Amurkawa da dama sun amince da hakan.