An yankewa Ante Gotovina hukucin dauri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ante Gotovina

An dai yankewa wani tsohon Janar din Croatia, Ante Gotovina, hukuncin dauri a gidan kaso na shekaru 24 bayan an same da aikata laifin yaki da kuma kashe sabiyawa a lokacin da aka raba Yugoslavia.

Kotun Manyan laifuka ta Majalisar dinkin duniya da ke Hague ta ce tsohon Janar din ne ya jagoranci wani kisan mumuken da aka yiwa Sabiyawa, sannan kuma aka kori wasu daga cikinsu a Yakin Krajina da ke Koreshiya a shekarar 1995.

Daruruwan 'yan kasar Koreshiya ne dai suka taru a babban dandalin tsakiyar Zagreb na cike da bacin rai da kuma rashin jin dadi lokacin da aka karanta hukuncin na kotun.

Suna dai kallon abinda ke wakana a Hague kai tsaye a lokacin da aka yankewa Ante Gotogna da kuma Maden Markach hukunci samunsu da aikata manyan laifukan da suka hada da kisan gilla tare da muzgunawa sabiyawan da aka kora daga Croatia a shekarar 1995.

Jama'ar dai na kada tutar koreshiya suna rera taken kasarsu, suna kuma rike da hotunan janar-janar din da har yanzu suke yiwa kallon wasu gwarazan 'yan kasa da suka 'yanto kasarsu.

Sun ce hukuncin kan abinda sukayi amanna da cewa wata halattacciyar gwagwarmaya ce ta 'yanta kasarsu, hukunci ne da aka dauka kan kasar baki daya.

Tuni dai aka shirya yin wasu jerin gwano na nuna kin amincewa da za'a yi gobe asabar, a yayinda mutanen dake tutiya da kasarsu suka turje kan abinda suka kira yaki don ceto kasar haihuwarsu.