INEC ta kammala shirin zaben Shugaban kasa

Image caption Shugaban hukumar zaben Najeriya, Attahiru Jega

A Najeriya, Hukumar zaben kasar ta ce ta kammala shiri don gudanar da zaben shugaban kasar da za a yi gobe Asabar. Hukumar ta bayyana cewa ta dauki kwararan matakai don magance wadansu matsalolin da ta ci karo da su a zaben `yan majalisar dokokin da ta gudanar a makon jiya. Wasu daga cikin matsalolin da ta fuskanta dai sun hada da jinkirin isar kayan zabe wasu mazabu, da zargin amfani da kudi da wasu `yan siyasar suka yi wajen sayen kuri`un jama`a da kuma malaman zabe da nufin sauya sakamakon zaben.

Mataimakin Daraktan hulda da jama`a na hukumar zaben Mr Nick Dazang ya ce hukumar ta koyi darasi daga ire-iren matsalolin da ta ci karo da su a lokacin zaben `yan majalisar dokokin kasar, kuma wannan ya sanya ta dauke matakan kauce musu a zaben shugaban kasar da za a yi gobe.

Zargin magudi

Wata matsalar da hukumar ta ce ta gano, ita ce ta zargin da aka yi cewar ana hada baki da jami`an hukumar wajen sauya sakamakon zabe, wato sakamakon da aka sanar a rumfar zabe daban, wanda kuma ake kaiwa gaba daban. Don haka ne ta jaddada tsarin leka sakamakon a rumfar zabe.

Shugaban kasar Ghana, kuma jagoran tawagar masu sa-idon a kan zaben Najeriyar ta kungiyar Tarayyar Afirka, Mr John Kuffour, wanda ya kai ziyara hukumar zaben Najeriyar, ya bayyana gamsuwa ga shirin hukumar zaben.

"Hukumar zaben Najeriya ta tabbatar mana cewar ta shirya wa zaben, kuma mana sa-ran za ta tabuka abin kirki wajen kai malaman zabe da kayan zabe, da jami`an tsaro.

"Lallai an fuskanci wasu matsaloli a baya, amma ga alama hukumar zaben ta dauki matakan magance su." In ji Mista Kuffour

Zaben shugaban kasar dai kawo yanzu sai hasashe ake yi game da yadda zai kasance.

Shugaban kasar mai ci na jama`iyyar PDP shi ma yana cikin takarar, yayin da sauran `yan takarar kusan goma sha takwas suka fito daga jam`iyyun adawa, ko da yake daga baya wasu sun yi janyewa, amma manyan jam`iyyun adawar su ne CPC da ACN da kuma ANPP.

Jam`iyya mai mulki ce ta samu rinjaye a zaben `yan majalisun dokokin da ya gabata, amma a wannan karon ra`ayin masu sharhi ya bambanta, saboda wasu na ganin jam`iyyar Pdp ce za ta sake samun galba saboda cijewar kawancen da jam`iyyun adawar suka so kullawa.

Sai dai wasu na ganin lamarin ka iya sauyawa har a kai ga zabe zagaye na biyu, saboda a zaben `yan majalisun dokokin a ra`ayin wasu, masu zabe a wurare da dama `yan takara suka zaba ba jam`iyya ba.