'Yan sandan Syria sun kabsa da masu zanga

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zanga-zanga ta fara bazuwa zuwa Damascus

Yan sanda a Syria sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kulake wurin tarwatsa taron masu zanga-zangar adawa da gwamnati da ke jerin gwano zuwa tsakiyar birnin Damascus.

wadanda abin ya faru gabansu sun ce 'yan sandan sun afkawa masu zanga-zangar ne lokacin da su ka tattaru a bayan garin Damascus da nufin kutsawa cikin tsakiyar birnin.

Dubunnan mutane ne dai su ka shiga zanga-zangar bayan sallar Juma'a a wasu garuruwan da ke fadin kasar.

Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun ce an kashe fiye da mutane dari biyu a yamutsin da aka dara wata guda a na yi.

Sai dai mahukunta sun ce fiye da talatin daga cikin wadanda su ka rasu 'yan sanda ne da sojoji.