Zaben Shugaban Najeriya

Image caption Zaben Shugaban Najeriya, kai tsaye

20: 19 A yanzu mun kawo karshen bayanan da muke kawo muku kai tsaye kan zaben shugaban Najeriya. Sai ku kasance damu a shirye-shiryenmu na radiyo, sannan kuma gobe idan Allah ya kaimu za mu kawo muku bayanai kan yadda sakamakon zaben zai kasance a shafin mu na bbchausa.com.

19: 50 A gaskiya talakan Najeriya yana bani mamaki, akoda yaushe zakaji yana cewa shugabanni na zaluntan su, amma da lokacin zabe ya yi sai kaga idan anbashi kudi kadan sai ya saida mutuncinsa. Shawarata itace dan allah talakan Najeriya ku kiyaye mutuncinku, yadda zai sa kaji dadin tsawon rayuwarka. Daga Adam Shekarau dan Nijar a Saudia Riyadh.

19:40 To mudai talakawa mun gama namu Allah ka ida mana sauran amin. Daga Sagir Adamu compound Malumfashi.

19:38 Jama'a cikin rana daya zamu ceci rayuwar mu ta shekaru hudu dan haka mu fito mu kasa mu tsare mu kuma raka. Sai mu barwa ubangiji. Daga: Kassim Abubakar Gamawa.

19:37 INEC mun kada kuri'un mu,sakamako kawai muke jira daga gare ki.ALLAH yasa karki bamu kunya.Daga Mansoor Said a jihar Kano.

19:34 Wakiliyar BBC a Maiduguri Bilkisu Babangida: A jihohin Borno da Yobe rahotanni na nuna cewar an kammala dukkannin zabubbukan cikin kwanciyar hankali duk da kuwa irin halin matsalar tsaron da aka fuskanta a jihar Bornon a jajibirin zaben da kuma safiyar yau na fashewar bama bamai.

19:30 Abdullahi Yusuf BBC Hausa Facebook: A mazabata (saidu zungur Primary school a Bauchi), mun kada kuri'a lafia kalau ba tashin hankali. An sa jami'an tsaro so sai a gurin, ba kamar yadda na ji a wasu mazabun ba. Na gani da idona ma'aikatan observer group na Ecowas, TUC, Police Commission,da wadan su.

19:24 Sade Saidu Daura BBC Hausa Facebook: Hakika anyi zabe lafiya. Damuwar mu itace bamu taba jin hukumar zabe ba ta hukunta wadanda aka kama da niyyar yin magudi ba.

17:57 Daga Zakariyya Musa Tela. Kano Mudai anan mazabar k/ruwa komai yana tafiya daidai ba tashin hankali. Allah yazabamana shugaba mafi alheri.

17: 56 Inayiwa 'yan uwana 'yan Najeriya fatan Allah yabamu shugaba nagari. Wanda zai tausayawa talakawa. Daga Naziru Kamilu Yakasai a Kano.

17:26 Aisha Umar BBC Hausa Facebook: Ni da mijina da tsohuwar cikina, da kuma dana, mun kada kuriar mu a mazabar mu dake bayan garin Gombe. Allah sa munyi a sa'a.

17:24 Sanusi Abdullahi BBC Hausa Facebook:A Garin Anglo-Jos matasa sun zargi wata jami'ar Inec da kokarin sayar da ragowar katin zabe,yanzu haka an kasa an tsare kuma za'a raka.

17:22 Nuraddeen Usman BBC Hausa Facebook: Ni dai zabe bai yi mani kyau ba, ba a tantance ni ba, ban samu jefa kuria ta ba.

17:20 Yakubu Abdullahi Geidam BBC Hausa Facebook: Akama wata mata da takardar jefa kuri'a 500 a Karamar hukumar Nufawa Bauchi. Kuma ankama wata mota da takardar jefa kuri'a inda aka dangwala wata jami'yya. Matasa sun sawa motar wuta. Allah kaci gaba da tona masu asiri.

17:17 Junaid Said BBC Hausa Facebook: Alhamdulilllahi! Na kada kuri'a ta cikin kwanciyar hankali da lumana,kuma a halin yanzu ina nan mazabata na kasa na tsare,har sai an gama kidaya kuri'u,sannan in raka.

17.12 An fara samu sakamakon zabe a wasu mazabu.

17:00 Mu dai a garin Jos Alhamdulillahi, zabe na gudana lami lafiya. Fatan mu shi ne, a bamu wanda mu ka zaba. Daga Alh. Inuwa Kwashe 'Yan haya Jos.

16:58 Zabe a nan Batagarawa low-cost Katsina state na tafiya cikin kwanciyar hankali babu wata matsala alhamdu-lillahi. Saminu Bako.

16: 54 Mun je rumfan zabe don ka da kuri'ar mu amma an hana mu, sunce sai PDP.Tahir saleh Bama. Daga Warri Delta state.

16:52 Mu na farin ciki a Katsina mun yi zabe a cikin kwanciyar hankali. Basiru Dan Dissi Katsina.

16: 49 Zaku iya kuma kallon hotunan tantance masu kada kuri'a ta wannan rariyar likau din http://www.bbc.co.uk/hausa/multimedia/2011/04/110416_pres_gallery.shtml.

16:39 Umaru Maibauchi BBC Hausa Facebook: Muna ci gaba da kada kuri'a anan unguwar Din kofar mai anguwa, wani yazo yana neman tada fitina yanaso yaja hankalin wasu da kudi amma ana cikin haka sai ga sojoji suka kamashi suka masa dukan kawo wuka suka tafi dashi.

16:29 Na kada tawa kuri'ar kuma zan tsaya har dare dan inji wa na zaba daga Aisha matar Muhd Ahmad Idris a kabuga Kano.

16:26 Bisa ga dukkan alamu talakawa mun fara gane gaskiya. Mu ci gaba da haka, mu nemi yancin mu. Wannan shi zai bamu shugabanni nagari. kada mu tsaya ana bamu kudi muna dangwalawa mungaye. Daga Hamisu Mohammed.

16:12 Sabiu Malami BBC Hausa Facebook: Na kada kuri'a ta lafiya kuma zabe na tafiya a mazabarmu FGGC Kazaure Allah ya taimake mu amin.

16:10 Ahmadu Manage Bauchi BBC Hausa Facebook: Matasa a garin bauchi primary na anguwar Borno sun hallaka wani barawon akwatin zabe wanda ake zargin an basu kudi ne.

16:09 Na sha rana da 'yata yar wata uku a baya, Allah ka sa jega ya bayyana min zabe na. Daga Fatima kokoko yola jihar Adamawa.

16:07 Umar Muhd Ferere BBC Hausa Facebook :Nima a ganin ido na naga ana rabawa musu kada kuri'a kudi a mazabata ta hotoron arewa kuma manya manyan mutane ne ke rabon kudin.

15:53 A kano, Mazabar Gama dake Karamar hukumar Nassarawa, mata sun bani mamaki. Kwalin ashana da maganin sauro kawai ake basu a canza masu ra'ayi. Daga Lawan Yakubu.

15:50 Wata mazaba dake mangwaron dan wayya Tudun Wada Kaduna wani ya yi amfani da kudi aman da kyar yasha. Daga Usman Kaduna.

15:48 Assalamu Alaikum mude a Kano municipal zaben mu har yanzu mutane sunyi yawa sosai a mazabar mu. kuma aikin baya tafiya. Daga Farouk Bashir Maifada.

15:42 A yau ne a kano a yankin gwale a wata mazaba a inda aka kama wata mata mai raba kudi a yayin da mutane suka gano ta tana raba kudi kuma a karshe aka yi mata dukan tsiya har sai da hukuma suka tafi da ita. Sako daga mai sauraron mu.

15:38 A daidai lokacin da mutane a jihar sokoto ke jefa kuri'unsu kwatsam sai gobara ta tashi a babbar kasuwar ta sokoto wanda ahalin yanzu wutar tananan tanaci. Daga Zayyanu Muhammad Sokoto.

15:38 Ibrahim Habib BBC Hausa Facebook: Muma dai a karamar hukumar Zaria ban Zazzau kofar gidan mai'anguwa, zabe yana gudana cikin lumana da kwanciyar hankali, domin talakawa sun fito yadda ya kamata kuma sun kada kuri'unsu, muna addu'a Allah ya zaba mana shuwagabanni nagari ameen.

15: 36 Muna samu labarin cewa babbar kasuwar Sakkwato ta kama da wuta.

15:34 Isah Zuru Mohammed BBC Hausa Facebook: Lallai muma 'yan garin manga dake karamar hukumar Mulki ta Zuru na zagaya kusan mazabu uku zuwa hudu, al'amarin sai dai ace Allah son barka, domin komai yana tafiya yadda yakamata saboda mazabu biyu daga ciki suna batun kammala zabensu, kamar rumfar dake Unguwar gujiya da kuma waddake a wata shiya mai suna Domo.

15:31 Abdoulsalam Tajudeen Alli BBC Hausa Facebook: Mun kada zabe cikin lumana a L.E.A Ja'afaru estate kabala costain Kaduna. Allah ya sa mudace amin.

15:29 Abdul Waisu BBC Hausa Facebook: Wai don Allah jama'a mai ya sa jami'an tsaro su ka yi karanci? Wallahi yau a katsina har zuwa yanzu banga soja koda dayaba. Bakamar wancan satinba.

15:28 Attahiru Hashimu BBC Hausa Facebook: Mazabun Bali da Gassol, a Taraba ta tsakiya, zabe yana tafiya gwanin sha'awa, duk wanda ya kada kuri'arsa yana murna.

15:24 Uzairu Yahaya Sunkuye BBC Hausa Facebook: Kaai! Gaskiya zabe sai hamdala saboda mun je mun jefa kuri'a a Kofar gidan Galaje a kofar ram a Jihar Bauchi hankali kwance, kuma muna gurin sai mun kasa mun tsare kuma mun raka.

15:20 To Alhamdulilahi mun fito mun zabi gwarzon saboda haka yanzu mun kasa muna tsare wa koma zamu raka don haka ina kira ga yan uwa na yan arewa da sufito su kada kuri'unsu. Aliyu Isma'ila Haruna, Gombe.

15:19 An kammala kada kuri'a a akwatin cikin nasara harma an bayyana sakamakon akwatin. Sai dai fatan Allah ya ba mu sa'a. Daga Musa umar mai nama Funtua.

15:17 An bada kudi a sayi kuri'a, abin harya zama ruwan dare, don muma a nan Kano muna kallo ana siyan kuri'a naira dari biyar ko dubu daya, kuma aksarin su matane. Daga Isah Musa.

15:13 Mu a jihar jigawa mutane basu fito sun yi zabe kamar yadda aka fito aka yi na 'yan majalisar dokoki da sanatoci. Don angama zaben karfe daya na rana saboda babu jama'a. Daga Bashir Abubakar.

15:11 A kaduna muna kada kuria kamar yadda ya kamata cikin 'yanci da walwala. Daga Hamisu Kargi.

15:05 Zaidu Bala Kofa Sabuwa BBC Hausa Facebook: Gaskiya Al'ummar Jihar kebbi kunci yabo da kun kaba hukumar zabe hadin kai don samun nasarar gudanarda zaben shugaban kasa a Najeriya, don yau gashi ana zabe a jihar kebbi babu satar akwatin zabe babu Magudi kuma babu coge.

15:03 Zabe na tafiya lafiya a katsina Kofar-soro. Allah ya sa a gama lafiya mu dai ba gudu ba ja da baya. Daga Jiddah.

14:56 Sadiq Tukur BBC Hausa Facebook: Wannan abu yana bamu takaici wallahi. Kullum cikin tsadar rayuwa muke, lokacin gyara yazo amma was saboda kudin shan ruwa suna saida yancin su. Wallahi da inada dama da na bar Najeria har abada. Kaico da wannan jahilci. Allah kawo mana dauki.

14:41 Hassan Kaoje BBC Hausa Facebook: Ni da kaina na gani da idona ana sayen kuri'a naira dubu daya a Sokoto.

14:40 An samu jinkirin fara zabe a karamar hukumar Suleja ta jihar Niger saboda rashin fitowar 'yan bautar kasa da aka horar domin aikin zaben. Musa Aliyu.

14:38 Babajo A. Bawa BBC Hausa Facebook: A mazabata da ke katirje Saminaka mai number 016 na zabi wanda na ke so saura sakamako ya rage Allah ka ba mu nasara ameen.

14:33 Mudai anan Argungu zabe yana tafiya yanda yakamata ba tashin hankali daga Haliru Rini Argungu.

14:32 Komi na tafiya lafiyau a mafiyawancin rumfunan dake cikin garin Jibia, a jihar katsina, kuma alamu na nunawa cewa za'a kammala zaben nan da wurwuri saboda yadda abubuwa ke tafiya cikin kwanciyar hankali. Muh'd Sayyadi Filin-Sale, Jibia.

14:28 Na yi farin cikin fitowar yan'uwana mata wajan zabe saboda neman 'yanci bana raguwa bane. Daga Fadima Ahmad a jihar Kano.

14:27 To Alhamdulillahi mun fito mun kada kuri'armu a cikin kwanciyar hankali da lumana, sai dai ba jami'in tsaro ko daya a gun sai dai talakawa ne suka kasa suka tsare da gaske saboda sun tanadi makamansu kamar su kokara akan shirin su na ko ta kwana daga masu satar akwati. Daga Muhammad Sagir Babaji Haske Azare jihar Bauchi.

14:25 Mudai katsina muna cikin matsalolin zabe, a mazabun Modoji Primary school har yanzu akwai inda ba'agama tantance masu zabe ba, kuma wasu mazabun fada kawai akeyi ba zaben ba. Mudai muna addu'a Allah yabamu shuwagabanni nagari. Daga Yusuf Buh.

14:23 A gaskiya zabe na tafiya lafiya a cikin garin Daura, Kowa na kada kuri'arsa cikin lumana da kwanciyar hankali. Daga Babangida Saleh Daura.

14:19 Cikin yardar Allah na kada kuri'a ta kuma aiki ya na tafiya cikin kwanciyar hankali domin al'umma sun fito musamman mata domin sun haura yadda suka fito a zaben baya. Muna rokon Allah kariyar sa akan duk wani magudi ko rashin gaskiya a wannan zabe, Allah ya bawa kasar mu zama lafiya kwanciyar hankali.Daga Nazifi Zubairu.

14:16 Mustapha Muhammad Kabir BBC Hausa Facebook: Wallahi an kusan kashe wanda ya zo daukar akwatin mazabar bitenary a garin Azare Jihar Bauchi. A sauran rumfuna kuwa mutane ne ke kare kuri'ar su.

14:03 'Yan Najeriya su yi zabe lafiya su kare lafiya, da fatan Allah ya basu shugaba na kirki mai tausayin talakawa. Daga Abdallah Sidi Thinta baraden jamhuriyar Nijar.

14:00 Sani Kabiru Sanin Baba BBC Hausa Facebook: Har yanzu ba'a fara zabe ba a mazabar Dorayi dake karamar hukumar Gwale Kano, saboda rashin kawo kayan zabe da wuri. Sai yanzu ne ake shirin farawa.

13:58 Gaskiya a nan Ringim, zabe yana tafiya yadda yakamata, sai dai tun jiya ake rabawa Talakawa kudi. Daga Suleiman Nasiru Illah.

13:56 Mudai zabe yana kankama a Chiranchi karamar hukumar Kumbotso jihar Kano, kuma muna layi zamu zabi ra'ayinmu. Daga Hafizu Bashir.

13:54 BBC ta shaida inda ake baiwa mata sabulun wanki da kudade domin su kada kuri'a ga wata jam'iyya jihar Kano. A wannan karon ba akan layi ake rabon ba, ana amfani ne da zaurukan gidajen da ke kusa da rumfunan zaben domin raba wa masu zabe musamman mata wadannan abububwan domin sauya musu ra'ayi kan wanda za su kada wa kuri'a. Wasu bayanai sun kuma nuna cewa an raba wa mazaje shinkafa inda wasunsu suka je gidajensu domin tursasa wa matansu lallai su kada kuri'a ga wadanda suka basu shinkafar.

13:53 Talakawa 'yan Najeriya ku kasa ku tsare ku kuma raka. Idan ba'a raka ba anan lalata take. Daga Fatima Yahaya Gwiwa lowcost Sokoto.

13:50 Abdussalam Salamwap BBC Hausa Facebook: Mu ma mutanen Lokoja jihar kogi muna nan muna kada kuri'unmu cikin kwanciyar hankali.

13:32 Allah ya wadaran talakan Najeriya mai saida yanci. Yanci bana rago bane. Indai haka zamu ci gaba da saida yancin mu wahala tukunnama. Daga Mansoor Said jihar Kano.

13: 29 An gama tantance masu kada kuri'a a nan Rumfar kofar fada a garin Pindiga, Jihar Gombe. Ba wata matsalar tsaro, kuma mutane sun fito fiye da wancan mako. Yanzu za'a fara kada kuri'a. Daga Kabir Idris Pindiga jihar Gombe.

13:27 Aminu Aliyu BBC Hausa Facebook: A gaskiya zabe na tafiya lami lafiya a mazabata dake Mbamoi word a Yola ta kudu, sai dai rashin fitowar jama'a sosai kamar zaben da ya wuce.

13:25 Zabe na tafiya yadda akeso sai har yanzu wasu kan zabi jam'iyyun da basu suke so ba saboda haka ya kamata a ci gaba da wayar da kan mutane kan yadda zasu zabi jam'iyyunsu. Daga Kabir Ahmad Tareewa kano.

13:22 A unguwar filin samji cikin Katsina har yanzu ba a fara zabe ba saboda dumbin mutane da ba a tantance ba da fatan Allah yazaban mana shugaba nagari mai kishin mu ameen. Daga Salim Adamu Bawa daga Jihar Katsina.

13:19 Kabeer Juniour BBC Hausa Facebook: Alhamdulillah. A mazabata dake 23 road Festac town Lagos nazo 11:30am aka tantance ni kuma karfe 12:13pm na kada kuri'a to yanzu haka ina gefe guda ina kallon ikon Allah.

13:17 Mu dai anan alhamdu illa zabe yana tafiya yadda yakamata, dan a yanzu iyayan mu sun manta da suyi zabe. Daga Aminu Garba Dogo, Azare Bauchi.

13:14 Sarkin Aljanun Fcbk BBC Hausa Facebook: A mazabar NNPC WARD dake Karamar Hukumar Tarauni dake Birnin Kano Akwatuna Masu lamba 09 da 010. Jama'a sun hallara su ma, kuma maganar tsari wato raba kudi babu.

13:12 Abubakar Yusuf Bello Mai'adua BBC Hausa Facebook: An tantance ni amma har yanzu ba'a fara zabe ba, a rumfa ta dake Ali Rumfar Zana a garin Mai'adua.

13:10 Muktar Bashir BBC Hausa Facebook: An fara baiwa mutane kudi a jihar Niger domin su zabi wata jam'iyya, ana bin masalatu da coci.

13:08 Janar Muhammadu Buhari, dan takarar Jam'iyyar CPC ya kada kuri'arsa a mazabarsa dake Daura a jihar Katsina.

13:04 Salihu Dauda Alhamdulillahi BBC Hausa Facebook: A hayin danyaro dake Samaru a Zaria, mun fara zabe da misalin karfe 12:30, kuma komai na gudana cikin kwanciyar hankali.

13:03 Kabeer Ahmad BBC Hausa Facebook: Zabe na tafiya kamar yadda ya kamata domin har na kada kuri'a ta a Mandawari. To amma fa har yanzu wasu nayin kuskure wajen zaben dan takarar da suke so.

13:01 Sadeeq Musa BBC Hausa Facebook:Muma anan mazabar Gobirawa Filin Durumi Kurna, karamar hukumar Dala Zabe yana tafiya lafiya.

12:56 Ibrahim Hassan Daraja BBC Hausa Facebook: Mu kam gaskiya anan Gusau jihar Zamfara a mazabar Layin Tudu a Tudun Wada muna fuskantar matsalolin rashin kwanciyar hankali, har yanzu ba a tantance rabin mutane ba. Nima dakyar aka tantance ni.

12:53 Mu dai a kontagora ma zabar Ataloli, sai muce sanbarka domin mun fito ga baki dayan mu domin jefa kuri'ar mu ga dan takaramu. Daga Ahmed Kontagora.

12:50 Dahiru (dan'bako) anguwar Maikafi, Bauchi. Muna nan mu na kada kuri'unmu cikin kwanciyar hankali.

12:45 Alhamdu lillahi na kada kuri'ata ,kuma ina fatan wanda na zaba in Allah ya bashi nasara , zai taimaka mana mu da 'ya 'yan mu da mazajenmu. Daga Aisha Mohammed kabuga Kano.

12:35 Shugaba Goodluck Jonathan ya kada kuri'arsa a kauyen Otueko dake jihar Bayelsa.

12:33 Hassan Muhammad Binanci BBC Hausa Facebook: An fara jefa kuri'a arumfa mai namba "002" da ke Unguwar magajin Garin sakkwato da misalin karfe 12: 10.sai dai wani abu da masu jefa kuri'a ke yi shi ne da zaran sunje jefa kuri'arsu sai sun kira sunan Allah mai girma kamin su kada.Da fatar Allah ka bamu sa'a.

12:30 MAIDUGURI: Bama-bamai biyu da suka tashi jiya da yau sun girgiza masu kada kuri'a a garin Maiduguri na jihar Borno. Sai dai babu rahotannin samun raunuka. Akwai dai jami'an tsaro masu yawa a ko'ina cikin birnin domin tabbatar da tsaro ga masu kada kuri'a. A cewar Mai Mamman. Kamfanin dilancin labarai na Reuters.

12:25 DAURA: Dubban jama'a ne suka taru domin ganin fitowar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC a mahaifarsa da ke Daura. Maza da mata sun fito domin a tantance su sannan su kada kuri'unsu. "Mun fito da wuri ne domin mu kada kuri'unmu. Mun amince cewa Buhari zai iya kawo sauyi mai inganci a kasarmu. A cewar Salisu Yahaya, dan shekaru 35. Kamfanin dilancin labarai na Reuters.

12:24 OTUOKE: A kauyen Otuoke, jama'a sun yi dogon layi a mazabar shugaba Goodluck Jonathan a karkashin wata rumfa da aka kafa.A cewar Elei Green, dan shekarau 45, da ya zo daga birnin Atlanta domin kada kuri'a. "Wannan ba wani kauye bane mai arziki. Muna murna yanzu daya daga cikinmu na da damar zama shugaban kasa. Wannan darasi ne ga matasa." Kamfanin dilancin labarai na Reuters.

12:21 Mu sakkwatawa gaskiya kudi basa rudar mu kan zaben wanda mu ke so, ba gudu ba jada baya. Inji Maharazu, Sokoto.

12:18 LAGOS: Jama'a sun fito da dama a birnin kasuwanci na Lagas. Dubban jama'a sun yi dogayen layi a mazabar Obalende da ke tsakiyar gari. "Na samu kwarin gwiwa kan abin da ya faru a makon da ya gabata, shi ya sa na fito wannan makon," a cewar Abubakar Labaran, wani tela da ya fito tare da matarsa da kuma 'yan'yansa biyu. Kamfanin dilancin labarai na Reuters.

12:16 ABUJA: An samu fitowar jama'a fiye makon da ya gabata. Jama'a sun fito da sassafe, domin hawa layi da kuma kada kuri'a.Tsohon Fira ministan Canada Joe Clark shi ne ke jagorantar tawagar masu sa'ido ta National Democratic Institute. Kuma ya ce "al'amura na tafiya kamar yadda ya kamata". Kamfanin dilancin labarai na Reuters.

12:08 Wakilin BBC, Ibrahim Isa a Abuja: Zaben dai za a iya cewa ya samu karbuwa a wajen jami`a, saboda galibin rumfunan zaben da na kewaya sun cika makil da masu zabe, wadanda suka sammaka domin a tantance su kana su kada kuri`unsu. Kuma na riski wasu da ke gardama a kan wanda ya riga wani shiga layin zabe.

12:05 Yahya Umar Bichi BBC Hausa Facebook: Gaskiya wannan zaben na shugaban kasa ba'a samu fitar jama'a sosai ba a rumfunan zabe daga yahaya umar bichi,jihar Kano.

12:02 Sani B Mohammed BBC Hausa Facebook: Alhamdulillahi mu dai nan Daura harkokin zabe komai yana tafiya yadda ya kamata.

12:01 Mu kam a Wukari, Taraba state sai hamdala domin jama'a sun fito kwansu da kwarkwata don kada kuri'a. Ba hayaniya ba tashin hankali. Daga Yusuf Adamu Abdullahi Bindige.

11.59 Bello Lawan Ibrahim BBC Hausa Facebook: Mu dai a mazabar Dangora karamar Kiru Kano zabe yana tafiya cikin kwanciyar hankali da lumana kuma jama'a sun fito sosai.

11.58 Hayat Abubakar BBC Hausa Facebook: Mu dai anan polling unit 26 dake Gbara Lekki Lagos ba wata matsala domin yanzu ina zuwa ko minti biyu banyi ba da zuwa na aka tantance ni. Sai dai alamu na nunawa mutane basu fito sosai ba.

11: 55 Mu dai nan fatakwol akwai 'yan mastaloli domin a mazabarmu ta layin Neja wani guri da ake kira Hausa layi sun zo sun ce mana lallai idan bamu zabi wata jam'iyya ba za su koremu. Daga Shaibu Sabo Fatakwol Hausa layi.

11.52 Mudai al'umar jahar Katsina cikin karamar hukumar Katsina, mazabar Kangiwa. Hukumar zabe bata cika al'kawarin data yiba na raba rumfunan zabe wuri biyu inda mutane suka wuce dari biyar, a mazabar Kangiwa akwai rumfar da keda mutane sama da dari takwas shi yasa satin da ya wuce wasu rumfunan har dare ba'a gama kada kuri'a ba. Daga Sada Tanimu Makeri Saulawa Katsina.

11.46 Samir Sani BBC Hausa Facebook: To mu dai a Chiranci Kumbotso Kano ana aiki sosai, sai dai layi yayi yawa a kowane akwati yanzu haka ba'a tantance ni ba.

11.42 BBC Hausa Facebook: Mu yan plateau mun fito kwan mu da kwarkwata akan mu kada kuri'armu. Kuma da alama za mu yi cikin kwanciyar hankali Allah ya ba mu sauyi ya kuma sa mu gama lafiya amin summa amin. Daga Musa Tasiu a garin jos, a jihar Plateau a Najeriya.

11.34 Shuaibu Yusuf BBC Hausa Facebook:Ni dai a nan mazaba ta, ungwan tudu zongo kataf komai na tafiya daidai.

11.32 Gaskiya abun kam sai hamdala domin komai yana tafiya daidai kawo yanzu har an gama tantance masu kada kuri'a a mazabar Audu Bature dake karamar hukumar Gamawa jihar bauchi. Allah ya mana zabi na gari. Daga: Kassim Abubakar Gamawa.

11.25 Suleiman Ndako Umar BBC Hausa Facebook: Tantance masu kada kuria na tafiya yadda ya kamata a Naharati Sabo primary school polling unit Abaji, karamar hukumar Abaji, Abuja. An fara tantancewar kafe 8 dedai. Matsalar da aka samu shine rashin sunayen wasu masu kada kuria a rajistar masu kada kuria. Ana sa ran jami'in zabe zaizo ya fadi abin yi.

11.22 Mu dai nan a Benin, jihar Edo aikin tantanci sunayen masu zabe natafiya lami lafiya a mazabata da ke aduwawa Big Joe Park. Malaman zabe sun zu dawuri. Daga Abdul Kadir Anas.

11.19 Mukan a Wukari,Taraba state sai hamdala domin jama'a sun fito kwansu da kwarkwata don kada kuri'ah. Ba hayaniya ba tashin hankali. Daga Yusif Adamu Abdullahi Bingide.

11.17 A yau assabar zaben shugaban kasa yanagudana kamar yadda yakamata mutane sunfito mata da maza domin suzabe abinda sukeso. A gaskiya 'yan matsalolinda anka fuskanta a zaben baya an magancesu musamman babbar matsalan nan ta bada kudi a runfunan zabe. Daga Zayyanu Muhammad Sokoto.

11.14 Mudai zamfara har yanzu yar gidan jiya muke domin suna amfani da kudi a rumfunan zabe. Shafiu Yuguda, Tsafe Zamfara.

11:07 Tantancewar da akai ta wancan zaben tasa an samu sauki a wannan karon daga mutum yaje za'a tantance shi domin akwai lambarsa da lambar shafinsa da aka lika a jikin rijistarsa. Basiru Shuaibu, karamar hukumar Gabasawa, Jihar Kano.

11.02 Alamu na nuna cewa za'a iya samun rikici da hargitsi a mazabar filin-sale cikin karamar hukumar Jibia a katsina, saboda matasan wata jam'iyya na neman taka dokokin zabe. Kuma har yanzu bata canja zane ba wajen rarrabar kudi daga yan siyasa. Don haka ana bukatar karin jami'an tsaro. Muh'd Sayyadi filin-sale, Jibia.

11:00 Muhammad Muhammad Yunus BBC Hausa Facebook: Mu a karamar hukumar Jere dake jihar Borno a mazabar Mashamari Rumfan block 6, ana tantance mutane kuma yana gudana lami lafiya Allah ya bamu zaman Lafiya.

10:55 Harda hawaye munyi dan bakin ciki akan wadanda suka saida mana da 'yancimu muna kira ga talakawa suji tsoran Allah sugane saida kuri'a tamkar saida rayuwace ta shekara hudu.Daga Hafizu Balarabe Gusau a Jihar Zamfara.

10. 53 Mu dai anan garin Kirenowa a karamar hukumar Marte, Jama'a basu fito sosai ba yan zu haka wasu rumfunan zabe ma'aikatan zabe ne kawai awajen .Daga SALEH MUHAMMAD TAHIR.

10.49 Mu dai anan komai yana tafiya daidai, sai kusan dukkan rumfunan zaben dana ziyarta a karamar hukumar Ondo ta kudu mutane basu fito sosai ba, jami'an zabe suna zaune suna jiran masu kada kuri'a suzo a tantance su. Daga Adamu Bello.

10.44 Abdullahi Mohd BBC Hausa Facebook: Kai Allah mai iko wai mutane me yake damunsu ne, yau gashi ana saida rijistar kada kuri'a Naira arbain. Allah yasa sawake.

10.42 Abin bakin ciki abin takaici wai har yanzu talaka bai daina siyar da 'yancinsa ba, marasa kishin harda dorawa kansu ganye suna tallan 'yancisu na shekara hudu. Daga Hafizu Balarabe a Gusau jihar Zamfara.

10.39 Gaskiya mu a akwati ta 21 dake Pambegua karamar hukumar Kubau dake jihar Kaduna har yanzu ba a kawo komai ba, babu kowa, ba jami'in zaben da ya zo bale a tantance mu. Auwal Ibrahim Pambeguwa.

10.34 Mu dai mazabun mu na karamar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna har yanzu babu jama'a sosai. Daga Aliyu k. Muh.d.

10:32 Tantancewa yana tafiya yadda ya kamata da zuwana ban wuce minti bakwai ba aka tantanceni a mazabar mu na Estate Ashaka siminti, Bage Ward karamar hukumar Funakaye, jihar Gombe, amman kash abin takaici Jama'a basu fito ba kamar na wancan satin, ubangiji Allah ya kyauta. Daga Musa Maty Ashaka.

10.26 A Yola jihar Adamawa wakilinmu Abdullahi Tasi'u Abubakar ya shaida mana cewa mutane da dama ba su ga sunayensu ba a rajistar masu kada kuri'a, da kuma karancin jami'an hukumar zabe da za su taimaka wajen gano inda matsalar take domin warwarewa. Kuma da alama mutane ba su fito sosai ba idan aka kwatanta da zaben da ya gabata.

10:24 Bello Muhammad BBC Hausa Facebook: Muna nan a Port Harcourt a cikin karamar hukumar Eleme ward 6 Eteo. An hana wasu kada kuri'a inda aka tilasta musu dole sai sun zabi wata jam'iyya.

10.18 An tantance dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar CPC Janar Muhammadu Buhari a mazabar shi dake Daura a jihar Katsina.

10.17 Chukwuemeka daga Obi Orodo kusa da garin Oweri jihar Imo ya kira BBC yana cewa, tuni aka kammala kada kuri'a a mazabar su, duk da cewa hukumar zabe ta ce sai karfe 12:30 za'a fara zabe.

10:14 Yanzu ina cikin layin tantancewa amma da alama har yanzu bata sake zani ba ga rajista amma kuma ba sunayan su a littafin tantancewa kamar yada ya faru azaben baya. Ya kamata suma asama musu mafita. Daga Nura Sharif Awaisu Tarauni Kano Najeriya.

10.11 Abba Tijjani Geidam BBC Hausa facebook: Abin mamaki anan garin geidam dake nan jihar yobe jama'a sunki fitowa dan tantance su, kamar ma ba ranar zabe ba, wallahi yanzu naje mazabata har an tantanceni saboda babu kowa awajen sai mutane daya daya.

10:07 A garin Maiduguri unguwar Galadima Junction, an samu tashin wani bam, amma babu labarin wani ya samu rauni, kuma jami'an tsaro sun yi ta harbe-harbe a sama, sannan an tsaurara matakan tsaro a garin. Wakiliyar tamu ta ce ta lura cewa ba a samu fitowar jama'a ba sosai kamar makon da ya gabata a wasu rumfunan zaben da ta leka.

10:06 Talakawan mu zabi mai gaskiya da rikon amana. Kar mutum yabamu kudi dan muzabi ra'ayinsa in dai muna bukatar canji a Najeriya kuma muna bukatan jin dadi da kwanciyar hankali a kasarmu sai munyi haka, Allah yabamu sa'a. Daga Telah Mai Oil karamar hukumar Gombi, daga jihar Adama

10.02 A mazabar garin Kusherki dake karamar hukumar Rafi ta jihar Naija, ba a kawo mana kayan zabe cikakku ba, inda misali wata mazaba da ke da kimanin mutane dubu daya, sai aka kawo dari hudu. In ji Ja'afar Kesherki.

10.00 Mu talakawa mun fita zabe manyan mu da yara, fatan mu shine a bawa wanda muka zaba. Abdulrazaq daga Azare Jihar Bauchi.

09:56 Wakilinmu Nura Ringim daga Kaduna ya ce an samu karancin kayan zabe a wasu mazabu, da kuma rashin zuwan ma'aikatan hukumar zabe a wasu mazabu. Sai dai an samu fitowar jama'a da dama a wasu wuraren ma fiye da na makon da ya gabata.

09:54 A gaskiya yadda zaben 'yan majalisar dokoki da na wakilai da ya gudana a jihar jigawa ya kawo nakasu ga jama'a wajen fitowa. Yau rumfunan zabe musamman a mazabar unguwar dake makarantar babale unguwar kakabori Hadejia domin da tantancewar zaben 'yan majalisu da ta yau duk kusan lokaci daya aka fara amma wajen gamawa sai gashi tantancewar yau ta kammalu da wuri fiye da na baya saboda rashin jama'a. sako daga Babangida chairman kakabori Hadejia jihar Jigawa.

09:52 An riga an tantance Shugaban kasa Goodluck Jonathan a mahaifarsa da ke Otuokwe jihar Bayelsa.

09:47 Farfesa Jega matsalar bacewar sunaye har yau tana nan ba mu ga wani mataki ba. In ji Kabiru S/Gari Gidan Irbo Birnin Magaji, Zamfara

09:37 Ya'u Abubakar daga rumfar zabe ta Mpape junction: "Yanzu ga ni nan tsaye a rumfar zabe amma an ce babu suna na a rajista, ga ni kuma da rajista ta a hannu. Jami'an zabe sun ce in jira."

09:36 Nura Zauro Abdullahi kuwa cewa ya yi, Yanzu ina nan na kasa na tsare a rumfar da nake aikin Party Agent, a gari na na Zauro, jihar Kebbi

09:34 Nura Mai Lemo daga Kano cewa ya yi, mu dai a yankinmu babu wata matsala kuma jama'a sun fito sosai.

09:32 Don Allah talakawa ku rabu da kudin yaudara, ku tsaya ku zabi mutumin kirki daga Alhaji Musa Lobanta Garke jihar Abia.