Za a janye dokar ta baci a Syria

Bashar al Assad an Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Bashar al Assad na fuskantar matsin lamba

Shugaban kasar Syria Bashar al Assad, ya bada sanarwar cewa dokar ta bacin da ta dade tana aiki a kasar, za a janye ta a makon gobe.

A cikin jawabin da ya yi ga sabuwar gwamnatin Syria da aka kafa wadda aka watsa ta kafar talabijin na kasar, shugaba Assad ya bayyana cewa:

"Mun kafa hukumar shari'a wadda ta gabatar da kuduri game da janye dokar ta bacin, bisa dokokin kasa da kasa.

"A gani na hukumar ta kammala aikinta a ranar Alhamis, kuma za ta bada shawarwari ga gwamnati, ta yadda za su zamanto doka ba tare da bata lokaci ba".