Ana tuhumar tsohon Firayim Ministan kasar Masar

Babban mai shigar da kara a Masar ya ce tsohon Prime Ministan kasar Ahmed Nazif da kuma wasu tsoffin ministoci biyu za su fuskanci tuhuma game da zargin amfani da kudaden jama'a ba bisa ka'ida ba.

Wani Jami'in gwamnati ya ce wannan tuhumar na da alaka da wasu kudade kimanin dala miliyan goma sha biyar da Mr. Nazif da Youssef Boutrous Ghali da kuma tsohon ministan kudi Habib Al Adli suka samu ta hanyar da bata dace ba.

Wakiliyar BBC ta ce masu bincike na duba wata kwangila ta kera lasisai na ma'aikatar cikin gidan da yawan kudin ya kai kimanin dala miliyan goma sha biyar