Abin da jama'a suka fi tattaunawa

Kate Middleton da Yarima William Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kate da William na jan hankalin jama'a sosai a Burtaniya

Bikin gidan sarautar Burtaniya na daga cikin abubuwan da aka fi tattaunawa tun lokacin da Yarima William ya sanar da aniyarsa ta aurar Kate Middleton.

Jaridun Burtaniya sun cika da hotunan masoyan biyu - wadanda suka yi karatu tare a jami'ar St Andrews tun lokacin da aka sanar da batun auren.

Kate Middleton ta zama abin kallo da kwaikwayo ta fuskar gashinta da kuma yanayin kayanta.

Sai dai kamar Diana, Gimbiyar Wales, kayayyakni da take sanya wa sun zamo abin tattaunawa a tsakanin jama'a.

Ganin yadda aka yi rige-rigen sayen kayanta na shirin bikin, akwai alamun za ta zamo wata abar koyi a fagen dinke-dinke da kuma kwalliya.

"Duk lokacin da wani babba a al'umma ya ke sanya wani tufafi a duniya, kuma wannan shi ne lokacinta, kuma duk abinda take sakawa babu shakka zai ja hankalin jama'a," a cewar Anna Wintour, babbar editan jaridar American Vogue.

An bayyana yanayin shigar Ms Middleton da cewa "mafi kyau, wanda jama'a ke sha'awa", kuma shi yasa kantina suke rububin kalar kayan na ta.