Shirye-shiryen bikin gidan sarautar Burtaniya

Kate Middleton da Yarima William Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption A ranar 29 ga watan Afrilu ne za a daura auren Kate Middleton da Yarima William

Amarya Kate Middleton da makusantanta za su kwana ne a jajiberen ranar daurin auren a babban Otel din Goring da ke Belgravia, a tsakiyar birnin London.

An kuma bayyana takamaiman lokaci da kuma hanyar da angwayen za su bi.

A bangare guda kuma Yarima Harry zai kasance tare da Miss Middleton a majami'ar Westminster Abbey, inda za ta auri Yarima William a ranar 29 ga watan Afrilu.

Harry shi ne ke bin bayan dan uwansa, kuma shi ne na biyu a masu jiran sarautar, kuma yana taka rawa sosai a bikin.

Za a bayyana addu'ar auren ne ga dubban jama'ar da suka taru a kan hanya ta bututun magana, da kuma dubban da ake saran za su saurari yadda angwayen za su gana da juna.

Za kuma a sanya manyan allunan kallo na zamani a Hyde Park da Trafalgar Square.