An kama shugaban 'yan adawa a Uganda

'Yan sanda a Uganda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da harba harsasai na roba don tarwatsa masu zanga-zanga dake nuna rashin jin dadinsu da kamun jagoran 'yan adawan kasar, Dr Kizza Besigye.

Haka ma an kama akalla wasu karin 'yan adawan su 12.

An tafi da Dr Besigye zuwa wani caji Ofis na 'yan sanda, bayan da ya yi yunkurin cigaba da kanfe din su na zuwa aiki a kafa, don nuna adawa da tsadar rayuwa a kasar.

A makon jiya ma' yan sanda sun tsare Dr Besigye da wasu karin 'yan adawan a lokacin wata zanga-zanga makamanciyar ta yau.

Haka ma hukumomin Ugandan sun yi kokarin toshe shafukan sada zumunta ta Intarnet.

Dr Besigye dai ya sha kaye a hannun shugaba Moseveni a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Febrairun da ya gabata.