Faransa ta yi gargadi kan sace 'yan kasarta

Wani Bature da aka sace a Mali
Image caption Wani Bature da aka sace a Mali

Gwamnatin Faransa ta gargadi 'yan kasarta cewa akwai hadari babba na yiwuwar a sace su a kasashen Mali da Nijar.

Karamin jakadan Faransa a Bamako, babban birnin Mali, shi ne ya fitar da wannan gargadi, yana cewa yana da sabon bayani, wanda ya sanya kara karfin hadarin yiwuwar sacewar.

An gargadi Faransawan da su kaurace ma yankin Mopti na kudu maso gabacin Malin, kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

A 'yan watannin dasuka wuce dai, kungiyar masu fafitika ta Al Qaida a yankin Maghrib, AQMI ta sha yin garkuwa da Turawa a Arewacin Jumhuriyar Nijar da kuma kasar Mali.