An dakatar da ministan cikin Gidan Najeriya

shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption shugaba Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya bada umurnin dakatar da ministan cikin gida na kasar, Captain Emmanuel Iheanacho daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.

Har wa yau ya dakatar da Mr Iheanacho a matsayin memba na majalisar zartarwa ta kasar.

An umurci Mr Iheanacho da ya mika ayyukan ma'aikatar ga ministan kwadago, Mr Emeka Wogu.

Shugaban dai bai fito karara ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki matakin a kan Mr Iheanacho ba.

Wannan al'ammari dai ya biyo bayan tarzomar da ta faru a sassa daban daban a Arewacin kasar game da zaben shugaba Jonathan.