An dage dokar ta baci a Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Masu zanga-zanga a Syria

Gwamnatin Syria, kamar yadda ta alkawarta, ta dage dokar ta bacin da take aiki da ita a kasar kusan tsawon shekaru hamsin.

Sai dai tare da hakan, ta bayyana wasu matakai da aka tsara da nufin daidaita yadda za a iya yin zanga-zanga a kasar, irin wadda yanzu ta game kasar. Ministan watsa labarai na Syriar, Adnan Mahmoud ne ya karanta sanarwar da ta kawo karshen aiki da dokar ta bacin ta tsawon shekaru arba'in da takwas.

Ya ce dokar da ta kawo karshen dokar ta bacin za ta tabbatar da tsaro da kuma mutuncin 'yan kasa.