Kotu ta tabbatar da takarar Aminu Bello Masari

Jam'iyyar CPC
Bayanan hoto,

Jam'iyyar CPC ta dade tana fama da rikicin cikin gida

Kotun daukaka kara a Nijeriya ta bayyana Alhaji Aminu Bello Masari a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar CPC a jihar Katsina, sannan ta ce babu dan takarar da ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar a Kano.

Sai dai Sanata Lado Dan Marke wanda kotun ta ce a yanzu ba shi ne dan takarar jam'iyyar CPCn a jihar Katsina ba, ya ce za su daukaka kara zuwa kotun koli.

A gefe daya kuma, Kotun ta yanke hukuncin cewa babu dan takarar da ya samu nasara a zaben fidda gwanin da jam'iyyar CPC ta gudanar a jihar Kano domin fidda dan takarar mukamin gwamna.

Sai dai a nata bangaren, hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ta ce za ta bayyana matsayinta a kan hukuncin kotun. Hukuncin kotun na yau dai ya soke wanda wata kotun tarayya ta bayar a baya, dake bayyana Sanata Garba Yakubu Lado a matsayin dan takarar jam'iyyar a jihar Katsina da kuma Alhaji Muhammad Abacha a matsayin takararta a Kano.