Faransa da Italiya za su tura dakaru zuwa Libya

Kasar Faransa da Italiya sun bi sawun Birtaniya wajen tura wasu jami'ansu domin su taimakawa 'yan tawayen Libya da shawarwari.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Faransa Francois Baroin ya ce, jami'an za su yi aiki ne da gwamnatin rikon kwarya ta 'yan adawa domin kare al'ummar farar hula.

Mr. Francois ya ce,"jami'an kadan ne wadanda za su yi aiki tare da gwamnatin rikon kwarya ta kasar domin su basu shawarwarin yanda zasu bi wajen kare al'ummar farar hula".

A jiya Talata ne ma Birtaniya ta ce zata tura da wata tawagar soji zuwa Bengazi, garin da 'yan adawa suka fi karfi.