Japan ta samu koma baya a harkokin kasuwancinta

Fira Ministan Japan Naoto Kan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wannan ne karon farko da kasar Japan ta samu koma baya dangane da irin kayayyakinta da take fitarwa, a cikin watanni goma sha shidda.

Gwamnatin kasar Japan ta ce, kayayyakin da kasar ke fitarwa zuwa kasashen ketare ya ragu da kashi biyu da digo biyu cikin dari a watan Maris, saboda tasirin mummunar girgizar kasa da tsunami da suka aukawa kasar.

Kasar Japan na daya daga cikin kasashen da ke da manyan kamfanoni masu fasaha sosai a duniya.

To amma yadda suke kera motoci da na'urorin lataroni, na farawa ne daga kananan masana'antun da iyalai ke kafawa a gidajensu wadanda ke samar da kayan hade hade.

To yanzu da tsunami ta lalata mafi yawa daga cikinsu, an samu gibin kayan harhada na'urorin lataronin.