Aminu Masari ne dan takarar CPC a Katsina

Alamar CPC Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Saura sasanta tsakanin magoya baya

Kotun daukaka kara a Nijeriya ta bayyana sunan Alhaji Aminu Bello Masari a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar CPC a jihar Katsina. Sai dai Sanata Yakubu Lado Dan Marke wanda kotun ta soke sunansa a matsayin dan takarar,ya ce zai daukaka kara zuwa kotun koli.

A gefe daya kuma, Kotun ta yanke hukuncin cewa babu dan takarar da ya samu nasara a zaben fidda gwanin da jam'iyyar CPC ta gudanar a jihar Kano na takarar gwamna.

Wannan hukunci ya soke wanda wata kotun ta bayar a baya, dake bayyana Alh Muhammad Abacha a matsayin dan takararta a Kano.

Jam'iyyar CPCn ta bakin mai ba ta shawara ta fuskar shari'a ta ce tana nazarin hukuncin, kafin ta bayyana matsayinta.