Zabe: Najeriya na fuskantar babban kalubale

Rikicin Zabe

Rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a Najeriya, ya nuna irin abubuwan da ka iya faruwa a kasar, ganin yadda bangarorin jama'a ke ci gaba da nisantar juna ta fuskoki dabam-daban.

Tashe-tashen hankulan da suka auku a a Arewacin kasar ya nuna cewa shugaba Goodluck Jonathan da shugabannin arewacin kasar na da babban kalubale a gabansu na ganin kasar ta ci gaba da zama wuri guda.

An kona gidaje da wuraren ibadar Musulmi da Kirista, kuma mutane da dama sun rasa rayukansu, lokacin da aka sanar da Jonathan a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Ko ta tabbata cewa an yi magudi ko kuma a'a, taswirar sakamakon zaben, ta nuna yadda kasar ta rabu gida biyu.

Buhari ya lashe kuri'u masu yawa a Arewa, yayin da Jonathan ya lashe dukkan na Kudancin kasar - duk da dai ya samu wasu kuri'un a Arewa.

"Wani lokacin akan nuna cewa babu maganar addini ko kabilanci, amma hakan na nan tsakanin jama'a a ko'ina cikin kasar," a cewar Mannir Dan-Ali, babban editan jaridar Daily Trust a Abuja.

An yi magudi Wani lokacin akan nuna cewa babu maganar addini ko kabilanci, amma hakan na nan tsakanin jama'a a ko'ina cikin kasar Mannir Dan Ali

Mutumin da hukumar zabe INEC ta ce shi ya zo na biyu a zaben shugaban kasar, Janar Muhammadu Buhari, ya ce an yi magudi sosai a zaben na ranar Asabar.

Ya ce akwai yankuna da dama da ba'a bar magoya bayansa sun kada kuri'a ba, musamman a Kudancin kasar.

Sai dai ya ce jam'iyyarsa za ta kalubalanci sakamakon zaben, sannan ya nemi jama'a da su kwantar da hankali.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce akalla mutane 35,000 lamarin ya raba da gidajensu a jihohi shida.

Majiyar 'yan sanda ta shaida wa BBC cewa akalla mutane 400 ne aka kama sakamakon rikicin a garin Kaduna.

Wakilin BBC Abdullahi Kaura Abubaka, ya ce al'amura sun fara komawa daidai a Kaduna.

Sai dai ya ce ana samun tashe-tashen hankula a Kudancin garin na Kaduna inda kirista suka fi rinjaye, amma an kara tura jami'an tsaro zuwa yankin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin ya biyo bayan zabe ne

A wani mataki kuma na nuna damuwa, fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa inda ta nemi kafafen yada labarai na kasashen waje da su daina bayyana yankunan kasar a matsayin na Kirista da Musulmai.

Wadanda rikicin ya fi shafa dai su ne 'yan kasuwar da ke hada-hada a bangarorin kasar daban-daban.

Masu fada aji

Fitattun 'yan siyasar da ke goyon bayan Jonathan sun fuskanci hare-hare.

Masu zanga-zangar sun kuma kai hari kan wadansu masu fada aji wadanda ake ganin na da hannun wajen koma bayan da yankin ke fuskanta idan aka kwatanta shi da Kudancin kasar.

"Wanann juyin juya hali ne. An kaiwa sarakuna hari, an kaiwa manyan mutane hari," a cewar Yinka Odumakin, mai magana da yawun Buhari, wanda ya yi suna wajen yaki da rashin da'a.

Akwai dai matsanancin talauci a Arewacin kasar, kuma akwai matasa da dama da suka hadar da zaman kashe wando. Su dai al'ummomin yankin da dama suna kallon Buhari a matsayin mutumin da zai iya kawo karshen halin da suka samu kansu a ciki.

Yankin Arewacin na fuskantar koma baya ta fannin talauci da rashin ilimi, karancin masana'antu da rashin aikin yi.

Baya ga wannan rushewar masana'antu - kamar masaku sakamakon shiga da kayayyaki daga China ya haifar da karuwar talauci a yankin - kamar yadda arzikin mai da sauran hada-hadar kasuwanci ta haifar da ci gaba a Kudu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar sakamakon zaben Najeriya