Jam'iyyar PDP ta yi Allah wadai da rigingimun bayan zabe

Farfesa Rufa'i Alkali, Kakakin jam'iyyar PDP mai mulki
Image caption Jam'iyyar PDP mai mulki ta bayyana nasararta da cewar nasara ce ga al'ummar kasar bakidaya dama damukradiyya kanta

A Najeriya, Jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ta yi Allahwadai da rigingimun da suka biyo bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar, wadanda ke ci gaba da haddasa asarar rayukan mutane da dukiya mai yawa.

Jam'iyyar ta ce kamata ya yi duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba, to ya garzaya ya nemi shari'a ta bi masa kadin hakkinsa maimakon tada yamutsi. Yace dole ne a cigaba da aiki da kotuna da kuma alkalai.

Kakakin jam'iyyar, Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali ya shaidawa BBC cewar babu wani cigaban da Najeriyar za ta samu a yanayi na tashin hankali.

Ya kara da cewar nasarar PDP, nasara ce ta kasa baki daya da kuma damukradiya kanta.

Dangane da janyo wasu jam'iyyun kuwa domin a dama dasu a cikin gwamnati, kakakin PDPn yace za'a dauki dukkan matakan daya dace domin a daidata al'umar kasa, a kuma zauna lafiya