Bam ya fashe a birnin Maiduguri

Taswirar Najeriya
Image caption An jefa wani bam akan wata motar 'yan sanda a babban birnin jahar Borno na Maiduguri

A Najeriya, rahotanni daga jihar Borno dake arewa maso gabacin kasar na nuna cewa, an jefa wani bam akan wata motar 'yan sanda a Maiduguri, babban birnin jihar.

Al'amarin dai ya auku ne cikin daren jiya, inda rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da jikkatar mutum guda.

Tun bayan murkushe kungiyar nan ta Boko Haram ne dai ake kai hare hare akan jami'an tsaro da 'yan siyasa, inda a yanzu salon kai hare haren ya sauya daga na bindiga zuwa tashin bama bamai.

Wakiliyar BBC a Maiduguri tace bam din ya tashi a unguwar Landan Ciki kuma tace an ji karar fashewarsa.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da tai ikirarin kai harin.