Majalisar koli ta sharia ta nuna damuwa

Wasu da  suka jikkata a tashin hankali a Kaduna Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu da suka jikkata a tashin hankali a Kaduna

Majalisar koli ta shari'a a Najeriya ta nuna damuwa a bisa halin da ake ciki a jahar Kaduna, musamman ma a kudancin jahar.

Ta ce duk da bayanan da jami'an tsaro ke bayarwa na cewa al'amurran sun lafa har yanzu ana halaka musulmi a wasu garuruwa na yankin.

Majalisar ta yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa na kai dauki ga wadanda ke cikin wani hali a yankin na kudancin Kaduna.

Jamian 'yan sanda dai sun musanta zargin,inda suka ce tuni aka kwantar da rikicin da ya farun a jahar ta kaduna,kuma abubuwa na komawa daidai.