Sojin Libya sun mika kansu ga hukumomin Tunisia

Rahotanni daga Tunisia sun ce sojojin Libya goma sha uku ne cikinsu harda wani Janar, suka mika kansu ga sojojin Tunisia dake kan iyaka, bayan fafatawa da 'yan adawar Libya.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayanin da aka bayar. Sai dai wadanda suka ga abin da idanunsu sun ce 'yan tawayen Libya sun karbe ikon iyakar da ta raba Tunisia da garin Dehiba.

Tuni dai kungiyar tsaro ta NATO ta musanta wani rahoto da kafar yada labaran Libyan ta fitar wanda ke nuni da cewa ta kai wani hari ta sama a garin Tarabulus wanda ya yi ajalin al'ummar farar hula bakwai da kuma raunata mutane da dama.