Kotun hukunta laifukan yaki za ta binciki rikicin zaben Najeriya

Moreno Ocampo Hakkin mallakar hoto AFP

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta laifukan yaki ta kasa-da kasa ICC Luis moreno-Ocampo, ya ce kotun tana binciken ko an aikata laifukan da suke cikin hurumin kotunsa ta yi bincike a kai, a rikice-rikicen da suka biyo bayan zaben shugaban Najeriya da aka gudanar ranar Asabar.

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta aike wa kafofin yada labarai.

Binciken da kotun ta duniya ke gudanarwa ya biyo bayan tarzomar da ta yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 100 ta kuma tilasta wa fiye da 40,000 suka bar gidajensu.

Tarzomar ta auku ne bayan sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC ta fitar ya nuna cewa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda ya fito daga kudancin kasar ne ya lashe zaben inda ya kayar da babban abokin hamayyar sa Janar Muhammadu Buhari wanda ya fito daga arewacin kasar.

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta laifukan yakin Luis Moreno Ocampo ya ce, kotun ta damu da rikice-rikicen da suka biyo bayan zaben, a don haka za ta bincika ko an aikata laifukan yaki a lokacin rikicin.

Shirya rikicin aka yi?

Ocampo ya ce ofishinsa na bin diddigin al'amuran da ke faruwa a Najeriyar, kuma ofishinsa zai bincika ko wasu ne suka shirya tashin hankalin kuma ko laifukan da aka aikata sun fada karkashin hurumin kotun binciken laifukan yakin.

Kotun hukunta laifukan yakin ta kuma kara da cewa zabukan gwamnonin da ke tafe a kasar ka iya tayar da sabbin rikice-rikice a kasar, a don haka ya yi gargadin cewa, duk wadanda ke da hannu a tada rikice-rikice don neman mulki, su kuka da kansu, domin doka za ta yi aiki a kansu.

Shi dai wannan binciken da kotun hukunta laifukan yakin ta duniya ke gudanarwa kan zaben Najeriya, yana mataki daya kasa da cikakken binciken hukunta laifukan yaki.

Kotun hukunta laifukan yakin ta kasa da kasa ICC wadda mazauninta ke birnin Hague, ita ce kotun duniya tilo mai zaman kanta da ke da hurumin bincika laifukan kisan kare dangi, da cin zarafin bil'adama da kuma laifukan yaki.

Kotun za ta bincika laifi ne idan kasar da aka aikata laifin a cikinta ta kasa hukunta wadanda ake zargi da aikata munanan laifukan yaki.

Ofishin mai binciken laifukan yakin dai a yanzu haka yana bincike a kan laifukan yakin da ake zargin an aikata a jihar Pilaton Najeriyar wadda ta sanya hannu a yarjejeniyar kafa kotun a shekarar 2001.