Jam'iyyun ANPP dana ACN sun hade a Jigawa

Taswirar Najeriya
Image caption Jam'iyyar ANPP a jahar Jigawa ta amince magoya bayanta su zabi jam'iyyar ACN a zaben gwamnan dake tafe

Yayinda ya rage 'yan kwanaki a gudanar da zabukan gwamnoni da na 'yan majalisar dokokin jihohi a Najeriya, jam'iyyun ANPP da ACN a jihar Jigawa dake arewacin najeriya sun kulla wata yarjejeniya inda ANPP ta amince magoya bayanta su zabi dan takarar kujerar gwamna na ACN maimakon nata,

Jam'iyyun suka ce sun yi hakan ne dai da nufin kwace mulkin jihar daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar da ma jihar a zaben gwamnan da za ayi

Haka kuma jam'iyyun sun ce suna cigaba da tattaunawa da jam'iyyar CPC, don itama ta shigo cikin wannan taron dangi.

Dan takarar gwamnan jahar karkashin jam'iyyar ta ANPP Barista Ibrahim Hassan Hadeja ya shaidawa BBC cewar jam'iyyarsu ta yanke wannan hukuncin, ta kuma baiwa ciyamominta umarni na cewar su fadakar da magoya bayansu cewar duk wanda zai zabi jam'iyyar ANPP a zaben gwamna, to yanzu ya jefa kuri'arsa ga dan takarar jam'iyyar ACN

Shima dan takarar gwamnan jahar karkashin jam'iyyar ta ACN Alhaji Muhammadu Badaru ya bayyana dalilin wannan kawance, inda yace sun duba yadda zabukan suke gudana ne, kuma suga ga ya kamata ace sun hada karfi waje guda domin gudun kada a rarraba kuri'u