Jama'ar Ivory Coast na cikin fargaba

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar bayar da agajin likitoci ta Medecins sans Frontieres, ta ce mutane a yammacin Ivory Coast na ci gaba da zama cikin tsoro duk kuwa kawo karshen rikici game da Shugabancin kasar.

Kungiyar ta MSF ta ce mutane na tsoron sojin sa kai da kuma ramuwar gayya, musamman a yankunan dake da dazuka kusa da kan iyaka da Liberia.

Ta ce mutane sun ci gaba da gujewa kauyukan da aka wasashe, aka kuma ragargaza, inda konannun gawarwaki suke baje kan hanya.

kungiyar ta MSF ta ce,suma sojin sa kai sun tsallaka kan iyaka domin kai hari a kan yan gudun hijirar Ivory Coast a cikin Liberia.