Japan zata gabatarwa majalisa kasafin kudi na gaggawa

Fira Ministan Japan Naoto Kan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamnatin Japan na bukatar dala biliyan hamsin domin aikin sake gina kasar cikin gaggawa

Gwamnatin Japan ta amince da kasafin kudin gaggawa na farko, wanda za a yi amfani da shi wurin aikin sake gina kasar biyo bayan girgizar kasa da tsunami.

Sai dai akwai bukatar dole sai majalisar dokokin kasar ta amince da kudaden da aka ware wadanda za su kai Yen Triliyan hudu, kwatankwacin dala biliyan hamsin kenan.

Japan tace zata yi amfani da wadannan kudade wajen gina gidaje na wucin gadi da sake gina tashohin ruwa da kuma tituna

Gwamnatin kasar dai tace ba zata karbi rancen kudaden ba a yanzu saboda dimbin bashin dake wuyanta

A madadin haka tace zata yi amfani da kudaden fansho da aka tara, da kuma zaftare kudaden da take kashewa a wasu fannonin.

Japan dai tace ta soke shirin da take yi na baiwa iyalai da yara kanana alawus-alawus, saboda ta samu kudaden da zata gudanar da aikin gyara kasar

Za'a gabatarwa da majalisar dokokin kasar wannan kasafin kudin kasa a mako mai zuwa