Karfin sojin Libya ya ragu da kashi 30

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban rundunonin sojin Amurka, Admiral Mike Mullen, ya ce harin sama da dakarun kawance ke kaiwa a kan dakarun sojin kasa na Libya ya rage karfinsu da kashi 30 zuwa 40 cikin dari.

Sai dai ya ce matakin sojin a Libya na kokarin cijewa.

Admiral Mullen ya kara da cewar bai ga wata alama ta hannun kungiyar Al -Qa'ida a cikin 'yan adawar Libya ba.

A halin yanzu daya daga cikin masu son ganin matakin sojin a Amurka, tsohon dan takarar Shugaban kasa, Sanata John McCain na a birnin Benghazi dake hannun 'yan adawa domin yin tattaunawa tare da shugabannin 'yan tawayen.

Jirage masu sarrafa kansu

Shugaba Obama ya umarci soma amfani da jiragen masu sarrafa kansu a wani bangare na farmakin da sojin kawancen NATO suke cigaba da kaiwa a kasar Libyan.

A lokacin da yake magana a Washington sakataren tsaron Amurkan Robert Gates, yace Amurkan zata samar da jiragen guda biyu makare da makamai masu linzami wadanda zasu rinka shawagi har na tsawon sa'oi ashirin da biyu a rana ga kungiyar NATO.

Jiragen zasu iya tashi kasa-kasa fiye da irin jiragen yakin da aka saba amfani dasu.

Sakataren tsaron yace babu wani abu sabo dangane da amfani da wadannan jiragen, illa iyaka cigaba da aka samu na zamani, kuma dama can yace an yi amfani da irinsu a kasar afganistan, akan 'yan tawayen Taliban.