Yakin da Amurka take yi da Libya ya sake daukar sabon salo

Jirgin yaki mai sarrafa kansa yana shawagi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka ta bada umarnin soma amfani da jiragen yaki masu sarrafa kansu domin murkushe dakarun Kanal Gaddafi a Libya

Shugaba Obama ne dai ya umarci soma amfani da jiragen masu sarrafa kansu a wani bangare na farmakin da sojin kawancen NATO suke cigaba da kaiwa a kasar libyan.

A lokacin da yake magana a washington sakataren tsaron Amurkan Robert gates yace Amurkan zata samar da jiragen guda biyu makare da makamai masu linzami wadanda zasu rinka shawagi har na tsawon sa'oi ashirin da biyu a rana ga kungiyar NATO.

Jiragen zasu iya tashi kasa-kasa fiye da irin jiragen yakin da aka saba amfani dasu.

Sakataren tsaron yace babu wani abu sabo dangane da amfani da wadannan jiragen, illa iyaka cigaba da aka samu na zamani, kuma dama can yace anyi amfani da irinsu a kasar afganistan, akan 'yan tawayen Taliban

To sai dai mataimakin ministan harkokin wajen kasar Libyan Khaled Kaim ya shaidawa BBC cewar amfani da irin wadannan jirage ba zai taimaka wajen kare fararen hula ba, illa iyaka ya sake dagula al'amura.

Ya kara da cewar yana tunanin a zauna a tattauna ta hanyar maslaha shine damukradiyya, amma ba turawa 'yan tawaye kudade ba, ko kuma makamai kamar yadda Amurkan take a yanzu.

Yace yana fatan Amurkan zata sauya shawara