Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Kalubalen dake gaban shugaba Jonathan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar, Najeriya Goodluck Jonathan

A Najeriya, sakamakon zaben shugaban kasa na ranar Asabar, ya janyo barkewar rikici a sassa daban daban na arewacin Nijeriya, lamarin da ya haddasa kona dukiyoyi da ma kashe kashe.

Su dai wadanda suka tada rigingimun suna zargin cewa an tafka magudi ne a zaben.

Hare haren da suka kai kan wasu al'umomi, ya sa a wurare irinsu Kudancin Kaduna, mazauna yankin sun kai hare haren daukar fansa wanda shi ma ya haddasa asarar rayuka da dukiya mai dimbin yawa.

Wannan batu dai ya sake sa wasu na tunanin cewa lallai an dawo da hannun agogo baya, a kokarin ganin kan kasa ya hadu, domin ciyar da ita gaba.

Wane kalubale ke gaban shugaba Goodluck Jonathan da aka bayyana cewar shi ya lashe zaben shugaban kasa, kuma wadanne darussa za a koya daga abin da ya farun? Wadannan da ma wasu al'amuran da zamu tattauna a shirin mu na Ra'ayi Riga na wannan makon.