An kashe masu zanga zanga fiye da 70 a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Akalla masu zanga zanga 200 suka mutu a Syria a 'yan makwannin nan

'Yan adawa masu fafutika a Syria sunce mutane fiye da 40 ne aka kashe a lokacin da dakarun tsaro suka bude wuta a kan masu zanga zangar neman demokuradiya a garuruwa da birane a ko'ina cikin kasar.

Wasu rahotanni sun ce yawan mutanen da suka mutun sun zarta haka matuka.

Dubun dubatar mutane ne dai suka hau kan tituna a mako na 5 na zanga zangar kin jinin gwamnati.

Duk da Shugaba Assad ya kawo karshen dokar ta baci a jiya alhamis, an tura dakarun tsaro masu yawan gaske gabanin sallar juma'a.

Rahotanni sun ce dakarun Syria sun budewa dubban masu zanga zanga wuta bayan sallar juma'a ne.

Wani wanda ya gani da idanunsa ya ce akalla mutane uku sun raunata a kusa da Damascus a yayinda rahotanni ke nuni da cewa an budewa masu zanga-zanga wuta a Homs da kuma Hama.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce akalla mutane 200 sun rasa rayukansu a zanga-zangar da aka gudanar a kasar a makwannin da suka wuce.