Libya ta dakatar da hari kan 'yan tawaye

'Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dakarun Libya zasu dakatar da kai hari kan 'yan tawaye

Dakarun gwamnatin Libya sun bayar da sanarwar dakatar da harin da suke kaiwa 'yan tawaye da ke rike da birnin Misrata.

Sai dai mataimakin ministan hulda da kasashen wajen Libyan, Khaled Khaim ya ce, dakarun gwamnati basu fice daga birnin Misratan ba, amma dai sun ba da dama ga shugabannin kabilun yankin sun gana da 'yan tawaye.

Amma wata majiya a Benghazi da ke da alaka ta kusa da Misrata ta ce, dukkan kabilun birnin na Misrata suna yakar dakarun Kanar Gaddafi ne, amma ba wai goyon bayanta ba.

A wani bangaren, Ministan hulda da kasashen wajen Libya, Abdul-Ati al-Obeidi yana kasar Tunisia, mai makwabtaka da Libyan. Rahotannin da ba a tabbatar ba dai na cewa, ministan yana kan hanyarsa ce ta zuwa kasar Cyprus, inda ya ce a watan jiya don tattaunawa akan yadda za'a kawo karshen rikicin na Libya.