Karancin nama a yankin Nija Delta

A yayin da wasu mabiya Addinin Kirista ,a fadin Duniya, ke bukin Ista, harkokin Kasuwancin Dabbobi na neman tsayawa cik, a wasu Jihohin da ke Kudu maso Kudanucin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan rikice-rikicen siyasa da addini ne da ake fama da su a wasu jihohin arewacin kasar, abinda ya kawo cikas ga kai dabbobi da ake yi zuwa kudancin kasar daga arewacin Najeriyar.

Al'ummomin yankin Naija Delta suna daukar bukin na Ista da muhimmanci, don haka wannan karancin dabbobi zai kawo cikas ga wannan buki.