Amurka ta zargi gwamnatin Syria

Masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka ta zargi gwamnatin Syria da yin amfani da karfin daya wuce kima akan masu zanga zanga

A yayinda al'ummar Syria ke shirin binne gawarwakin mutanen da aka kashe, a ranar da aka fi zub da jini cikin mako guda da aka kwashe da soma rikici a kasar, Amurka ta zargi gwamnatin Syria da amfani da karfi fiye da kima akan masu zanga zangar lumana.

Shugaba Obama na Amurkan ya ce yayi Allah wadai da tashin hankalin na ranar jumu'a, inda mutane fiye da saba'in suka rasu.

Sai dai wasu a Syrian sun zargi masu zanga zangar da tada zaune tsaye.

Wani ma'aikacin kwana kwana da aka nuna a kafar talabijin din kasar yace wannan harbe harbe ne da suka nuna karara cewa mutanen ba wai 'yanci suke nema ba illa iyaka yace so kawai suke su lalata kasa tare da durkusar da ita.